Assalamu alaikum. Ina fatan wannan saƙon zai same ku lafiya.
Muna so mu ja hankalinku kan matsanancin halin da makarantu ke ciki a yankinmu. Gidajen karatu da yawa sun lalace, bulo na fadowa, rufin bulo ya karye, ba kujeru ga ɗalibai, kuma babu ingantaccen ruwa ko bandaki. Wannan yana barazana ga rayuwar yara da kuma makomar iliminsu.
Muna roƙon ku da ku ɗauki mataki cikin gaggawa domin ganin an gyara makarantu a yankinmu. Muna fatan za ku tsaya tsayin daka wajen kare hakkokin ‘yan yankinku, musamman yara masu neman ilimi.
Na gode da kulawarku da kuma sadaukarwarku wajen inganta rayuwar al’umma.
Nagode kwarai,